Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Dan Takarar Shugabancin Kasa A Nigeria Atiku Ya Garzaya Kotun KoliRahotanni da ke fitowa daga tarayar Nigeria sun bayyana cewa Alh Atiku Abubakar Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP , ya garzaya Kotun Koli, domin kalublantar shari’ar da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta yanke na tabbatar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya samu nasara a zaben 2019 da aka gudanar.

Daya daga cikin manyan lauyoyin Atiku, wato Mike Ozekhome, ya bayyana cewa dalilai 66 ne suka sanyaya daukaka kara zuwa Kotun Koli domin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke da suka ce an tafka kurakurai. 

A ranar 11 Ga Satumba ne Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, a karkashin Shugabancin Babban Mai Shari’a Mohammed Garba, ta bai wa Buhari da APC nasara a kan Atiku da PDP.

Kotun ta ce Atiku da PDP sun kasa gabatar da hujjojin da za su gamsar da ita da cewa an yi magudi a zaben, daek nuna cewa shi ne ya yi nasara, kamar yaddaPDP din ta nemi kotun ta zartar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu