A Aljeriya, jarirai takwas ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu a wata gobara data tashi a wani asibiti dake gabashin kasar.

Gobarar dai ta tashi ne a cikin asibitin na lardin El-Oued a wajajen karfe 04:00 na dare agogon wurin,kamar yadda gidan talabijin na Channel 3 ya rawaito.

Firaministan kasar, Noureddine Bedoui, ya bukaci da a gudanar da binciken gaggawa kan gobarar, tare da baiwa ministan kiwan lafiya na kasar umarnin ya je asibitin da lamarin ya faru domin gani da ido.

Kakakin hukumar agajin gaggawa ta kasar, ya ce, an yi nasara ceto jarirai 11 da kuma mata 107 yayin gobarar data kama asibitin.