Shugabar kasar Habasha ko Ethiopia ta maida martani ga tokoranta na kasar masar dangane da gina madatsar ruwa ta Annahdha kan kogin nilu a kasar.

Shafin yanar gizo ta Africa news ya nakalto Sahle-Work Zewde tana fadar haka a jawabin da ta gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya a ranar 26 ga watan Satumba da muke ciki.

Kafin jawabinta dai shugaban kasar Masar Abdul Fattah Assisi ya fadawa taron shuwagabannink kasashen duniya kan cewa batun ruwan konin Nilu, batun rayuwa ne ga mutanen kasar Masar.

Amma Sahle-Work Zewde ta fadawa shuwagabannin kan cewa batun kogin nilu bai kamata ya zama al-amari na rashin fahinta a tsakanin kasashen da kogin ya ratsa cikinsu ba.

Ta kuma kara da cewa madatsar ruwa ta Annahdah, wata babban dama ce ga dukkan kasashen da kogin ya ratsa a ciknsu, na su yi amfanin da ruwanta.

Kasashen Masar ta Habasha dai sun kasa fahintar juna dangane da shirin kasar Habasha na gina madatsar ruwa kan kogin nilu wanda hakan zai iya rage yawan ruwan kogin da zai isa kasar Masar.

Daga karshen Sahle-Work Zewde ta kara jaddada cewa kasar Habasha zata yi kokarin ganin ta kai ga fahintar juna tsakaninta da kasashen Sudan da Masar dangane gina madatsar ruwaa kan kogin Nilu.