Wasu hare-hare da jiragen yakin gwamnatin Saudiyya suka kaddamar da safiyar yau a yankin Sawad da ke cikin gundumar Umran a kasar Yemen ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 5.

Tashar talabijin ta Almasirah daga kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau jiragen yakin masarautar Saudiyya sun yi ruwan bama-bamai a yankin Sauda, inda suka ragargaza wani masallaci a kauyen, inda suka kashe fararen hula 5 dukkaninsu iyalan gidan guda.

Rahoton ya ce mutanen sun fito daga cikin gidansu ne suka fake acikin domin kaucewa hare-haren jiragen yakin na Saudiya, amma kuma jiragen suka harba makamai a kan masallacin, wanda hakan ya ragargaza ginin masallacin tare da kashe mutane da ke ciki, da suka hada har da kananan yara guda biyu.

Wannan na daga cikin irin hare-haren da Saudiyya ta kwashe tsawon kimanin shekaru biyar tana kaddamarwaa kan al’ummar kasar Yemen, inda ta kashe dubban fararen hula kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tabbatar.
A halin yanzu mayakan sa kai na kasar Yemen sun fara mayar da martani kan irin wadannan hare-hare, martanin baya-bayan nan shi ne wanda suka kaddamar kan kamfanin mai na Aramco na kasar Saudiyya, wanda ya yi sanadiyayr mayar da man da kasar take fitarwa zuwa kasa da rabi ahalin yanzu.