Wani jami’in gwamnatin kasar Rasha ya bada sanarwar cewa kasar ta Rasha da kuma Iran zasu samar da wata kafa ta musayar kudade tsakanin kasashen biyu wanda zai bawa yan kasuwa damar kaucewa takunkuman da wasu kasashe suka dora masu na harkokin bankuna.

Tashar talabijinn ta Presstv ta nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaban kasar ta Rasha shawara kan al-amuran tattalin arziki yana fadar haka a birnin Moscow.

Ushakov ya kara da cewa kasashen biyu zasu aiwatar da wannan shirin ne ta hanyar samar da hanyar hada tsarin musayar kudade tsakanin bankuna a cikin kasar Iran wanda ake kira SEPAM da kuma bankunan kasar Rasha.

Ta wannan hanyar ce za a rika biyan kudade da kuma harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ba tare da shiga tsakani na kudaden wasu kasashe ba.

Tun shekara ta 2017 ne kasar Amurka ta hana bankunan Iran yin amfani da kafar musayar kudade tsakanin bankuna fiye da 200 a duniya, wanda ake kira SWIF.
Haka ma kasar Rasha tana fuskantar irin wannan matsalar saboda rikicinta da kasashen yamma kan kasar Ukraine da Crimea.