Ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawad Azrif tare da wakiliyar tarayyar turai akan harkokin waje da kuma tsaro. 

Federica Mogherini sun yi bitar hanyoyin da za a aiki da su domin kare yarjejeniyar Nukiliyar da aka fi sani da (JCPA) a takaice.
Bangarorin biyu sun yi ganawa ne a bayan taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 da ake yi a birnin New York. 

Wannan taron ya zo ne jim kadan da wasu kasashen turai suka fitar da sanarwa suna masu yin kira da a sake kulla wata sabuwar yarjejeniyar wacce za ta kunshi batun Nukiliya da kuma na tsaro a yankin gabas ta tsakiya.

Iran ta mayar da martani da cewa; Babu batun kulla wata sabuwar yarjejeniya gabanin a yi aiki da dukkanin ka’idojin da wacce ake da ita a yanzu ta kunsa.
A gobe Laraba ne dai shugaban kasar Iran da ministan harkokin waje, Muhammad Jawad Zarif za su gabatar da jawabi a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya