A ranar farko ta makon tsaron kasa, dakarun tsaron kasar Iran sun nuna sabin makaman kariya da suka kera.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya labarta cewa a jiya Lahadi, yayin da ake bikin makon tsaron kasar, dakarun tsaron kasar sun nuna sabin makaman kariya da suka hada da makamin kariya na Artillery da suka bashi sunan Ha'el a kusa da hubbarin marigayi Imam Khumaini wanda ya kafa jamhoriyar musulinci ta Iran.

shi dai wannan makami ta Artillery mai lakabin Ha'el makami na kariya mai dauke da rada-rada da albusai masu yawa, yana da karfin kakkabo makaman linzami da ake harbo ko kuma jirgin yaki maras matuki, kuma cikin sauki zai iya gano duk wani makami da aka harbo cikin kasar tare da kakkabo shi, ba tare da shi kuma an ganshi wurin da yake ba, har wa yau shi wannan makami, makami ne na tafe da gidanka ba irin wanda ake ajiye a wuri guda ba ne.
Har ila yau dakarun tsaron kasar ta Iran sun nuna wani sabon jirgin yaki maras matuki samfarin Kaman 12, wanda yake da karfin daukan bama-bamai masu yawan kilograme 100, kuma a tsahon awa daya na iya cin zangon kilimita 160.

Har ila yau an nuna wasu sabin makaman kariya da suka hada da makami mai linzami samfarin Asr 67 , da Asif da sauran makaman kariya da dakarun tsaron suka kera.