Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya yi watsi da zargin da kasahen turai sukayi wa kasarsa na cewa tana da hannu a harin da 'yan Houtsis na Yemen suka kai wa kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya.

Shugaba Rohanin ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, a daura da babban taron MDD, a birnin New York, inda ya bayyana cewa zargin na kasashen da suka hada da Faransa, Jamus da kuma Biritaniya, bai da tushe.

A jiya ne Kasashen Faransa, da Jamus da kuma Biritaniya, suka bi sahun Amurka da Saudiyya, wajen zargin Iran da hannu da harin da ‘yan Houtsis na Yemen suka kai kan tashohin mai mafi girma na duniya na kamfanin ARAMCO na Saudiyya.

A wata sanarwar bai daya da suka fitar ranar Litini din nan, bangarorin da suka hada da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma fira ministan Biritaniya Boris Johnson, sun dora alhakin harin da aka kai wa Saudiyya a ranar 14 ga watan Satumba nan ga aksar Iran.

Kasashen wadanda suka bayyana hakan a wata ganawa daura da taron koli na MDD, dake gudanar a birnin New York, sun ce babu wata makawa Iran ce ke da hannu a harin.

Kasashen sun kuma bukaci kasar ta Iran data kaucewa duk wata sabuwar tsokana.

Iran dai na mai ci gaba da musanta zargin, tana mai cewa goyan bayan siyasa ne take baiwa ‘yan Houtsis na kasar ta Yemen, hasali ma abunda ya faru ga Saudiyya fansa ce ta farmakin shekaru biyar da Saudiyya da kawayenta ke kaiwa ba kakkautawa akan kasar ta Yemen, wanda ya hallaka dubban fararen hula galibi mata da yara.