Kwamadan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, Manjo Janar Husain Salami ne ya bayyana haka a jiya Asabar a wajen baje kolin jirage marasa matuki daban-daban Manjo Janar Salami ya kara da cewa; Baje kolin yana nuni ne da wani nau’i, kadan na ci gaban da aka samu a fagen fasahar zamani.

A nashi gefen, kwamandan rundunar saman dakarun kare juyin musulunci na Iran, manjo janar Haji Zadah, ya ce; Iran tana da jirage marasa matuki da suke dauke da ci gaba na karshe da ake da shi a duniya.

Kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa; Za mu kai hari akan duk wanda ya ketaro iyakokin kasarmu, wannan sako ne bayyananne, muna kuma sanar da shi a fili.
Manjo Janar Salami ya yi ishara da yadda makiya su ka dunkule wuri guda domin cutar da al’ummarIran domin durkusar da ita, sannan ya ce; Sai dai akasin abin da suke so ne ya faru, domin jajurcewar al’ummar Iran ce ta sami galaba