Shugaban hukumar shiga da fita ta kasar Najeriya Muhammad Babandede ya bayyana cewa; Babu ja da baya a cigaba da rufe kan iyakokin kasar da aka yi, yana mai kara da cewa matakin da aka dauka ya haifar da ‘da, mai ido ta fuskar tsaro.

Babandede wanda ya bayyana haka jiya a kano ya kara da cewa; babu wata kasa wacce ta san abin da take yi wacce za ta bar kan iyakokin sakaka ba tare da daukar matakan hana shigar da kayan fasakwauri ba.

Babandede ya kuma ce; aikin jmai’an shiga da fice shi ne su tabbatar da tsaro akan iyakoki idan kuma ba haka ba, to za a rika fada da masu aikata laifuka a cikin kasar.
A kamon da ya wuce jami’an shiga da ficen sun kashe tare da kame wasu mutane da suke dauke da kayan laifuka, sannan kuma su ka ki yarda da a bincike su.

Daga cikin kayan da aka samu a tare da mutanen da akwai kananan binidgogi, wayoyi da kananan kwamfotoci, ba tare da takardun dake tabbatar da mallakarsu ba.