Rahotanni da suke fitowa daga Masar sun ce mutum na bayan nan da aka kama shi ne Alaa Abdel Fattah, a yau Lahadi.

Abdel-Fattah ya yi fice a kasar Masar saboda rawar da ya taka a lokacin juyin juya halin kasar a shekarar 2011 wanda ya kai ga kifar da gwmanatin shugaba Husni Mubarak.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya mabato mahaifiyar Abdel –Fattah, Laila Soueif tana cewa an kama dan nata ne a yankin Dokki dake cikin birnin alkahira.

Jami’an tsaron sun sanar da kame Abdel-Fattah ne bayan da su ka gayyace shi domin amsa tambayoyin Kwanaki biyu da suka gabata ma dai jami’an tsaron na kasar Masar sun kame masu fafutuka da dama da suka hada da malaman jami’a da masu 

fafutukar kare hakkin yin Zanga-zanga.
Makwanni biyu da su ka gabata ne dai aka fara gudanar da Zanga-zangar yin kira ga shugaba Abdul Fattah al-Sisy da ya yi murabus, wacce wani dan kwangila muhammadu Ali ya kira yi mutanen kasa