Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

JAMI'AN TSARO SUN BUDEMA WUTA A WAJAN MUZAHARAN ASHURA A KADUNAA safiyar yau Talata 10/9/2019 Da misalin karfe 6:00am ne Yan uwa Almajiran Sayyed Zakzaky na Kaduna suka fito muzaharan Ashura domin Tunawa da Shahadar imam Hussain (as) a Karbala Muzaharan wacce aka saba yi duk shekara, sai dai tun bayan kisan zalunci da ta'addancin sojojin najeriya suka aikata a kan 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya (Islamic Movement in Nigeria) a watan Disambar ranar 12/12/2015, mu ke fuskantar ta kura, cin zarafi da wulakanci, daga jami'an tsaron kasar nan, karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta han yar take mana hakkin mu, da hana mu yin addini yadda muka fahimta a matsayin na 'yan Nigeria, haka al'amarin yake tafiya, jami'an tsaro na kai hare-hare a kan mu lokaci bayan lokaci, a kan mu, a lokutan muzaharori da sauran munasabobi. 

I dan mai karatu bai manta ba, a jiya 9/9/2019 mun saki rahoton da muka samu na shirin  Jami'an tsaro na zubar da jinin almajiran Sheikh Zakzaky a manyan baranen kasar nan, Kaduna Katsina Kano bauchi, to sun aikata hakan a garin kaduna yayin da zuka zo da muggan makamai suka aukawa aukawa almajiran Malam Zakzaky a garin Kaduna.

To irin wannan nuna fin karfi da take mana hakkin mu, da jami'an tsaron shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi, Lallai ba zai haifar da na tija ba illa kara mana azama. Domin zanga-zanga ce ta neman ayi adalci adaina zalunci  Na tabbata ba wani ɗan adam ma'abocin hankali da yake son wanzuwar zalunci.

Bilhasali ma umarni ne na mahaliccin mu a tsayar da adalci a cikin al'umma wanda shine dalilin aiko Annabawa da Manzanni. Aikin da Imam Mahdi (AF) zai ƙarƙare shi nan ba da daɗewa ba. Dukkan masu ƙyamar zalunci a ƙasarmu su shirya dan tarbar wannan lokacin in yazo na yin arangama a tsakanin masu son adalci da masu ƙaunar ayi zalunci. Zanga zanga ce wacce an riga anyi mata key tun a 2015 a garin Zaria.


Muzaharar ta daga ne a hayan dan mani dake kan titin bye pass anan cikin garin Kaduna da misalin karfe 06:00am, amma dubai ne suka fito masu kaunar adalci, a yayin da rundunar shaidan masu kauna zalunci suka fito suka kashe mutane uku (3) da raunata da dama.


KNPRSCD 07
Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu