Harkar Musulunci a najeriya karkashin Sheikh Ibraheem Zakzaky, mun barranta daga dukkan wani nau'i na ta'addanci da tashin hankali.

Bayan mummunan harin ta'addanci da Jami'an tsaron 'yan sandan Najeriya sun kaiwa 'yan uwa musulmi almajiran shekh Ibrahim Yakuba El-Zakzaky, a ranar 10-9-2019 hari yayin da muke gudanar da traron Ashura a yankuna daban-daban na kasar, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan akalla mutune 17 da kuma jikkata wasu da dama na daban.

Sai ga shi a safiyar yau 13-9-2019 mun wayi gari da bakon labari a cikin garin Kaduna, yayin da civil defense na bi makarantu boko, suna sa a kulle wai a kwai wani abu da zai faru a yau a kaduna, a cewar su wai mabiya mazhabar Ahlul Baiti (As) Harka Musulunci a Najeriya wai za su dauki fansa a kan abin da ya faru ranar Ashura.

A gefe guda kuma mun tuntubi hukumar gudanar da tsarin karatun primary da secondary na jahar Kaduna sun shaida mana cewa, su suka bada umarnin kulle dukkan wata makaranta da suka koma karatu saboda a cewar su akwai sauran hutun zango wanda bai kai ga qarewa ba

To koma dai mene ne... A tsawon shekaru arba'in (40) da yan kai na da'awar Sheikh Zakzaky harkar musulunci a najeriya bamu taba daukar doka a hannun mu ba, balanta mu yi ramuwar gayya, ko ba komai Al'umma shaida ne a kan al'amarin waki'ar Zaria 12/12/2015 yadda rundunar sojojin kasar nan suka dira a kan mu, suka kashe sama da dubu 1000+ da kama malamin mu, wanda haryanzu gwamnatin Najeriya na tsare da shi, amma ba mu yi ramuwar gayya ba.

Dan haka muna kira ga al'ummar kasar nan, da su sani bamu da alhaki a kan duk wani ta'addaci da suka ga ya faru a wannan kasar, su zargi jami'an tsaron kasar nan da gwamnati. Su ke kisa, su ke yada farfa ganda a cikin al'umma.

Sa hannu Dandalin Media Forum na harka islamiya reshan jahar kaduna.