Hukumoni a jamhuriyar Kamaru sunyi watsi da rahoton cewa sojojin kasar na amfani da haramtatun hanyoyin wajen azabtar da jama’a a yankuna biyu na kudu da yammacin kasar masu magana da harshen turancin ingilishi.

A ranar 19 ga watan Satumban nan ne, shaffin yada labaran faransa na Mediapart, ya rawaito cewa sojojin na Kamaru na amfani da salo na azabtarwa na kasashen Faransa, Amurka da kuma Israila, irin na lokacin yake-yake da suka faru shekaru aru-aru da suka gabata.

Da yake maida martini kan batun, ministan sadarwa na kasar ta Kamaru, René Emmanuel Sadi, ya ce babu kashin gaskia ko kadan a rahoton.

Ya kara da cewa zarge zargen da ake na cewa, Kamaru ta tanadi wuraren azabtar da jama’a na sirri, da kuma daukar matakan da suka kaucewa shari’a da amfani da karfi fiye da kima na jami’an tsaro kan fararen hula ba gaskiya ba ne.