Gwamnatocin kasashen Najeriya, Nijar da kuma Chadi, suna shirin fara aiwatar da wani shiri na hadin gwiwa a tsakaninsu domin inganta ayyukan noma.

Shugaban hukumar yaki da kwararowar Hamada a Najeriya ne ya bayyana hakan a taron kare Muhalli da ke gudana a kasar India, inda ya bayyana cewa; a halin yanzu kasashen da suke makwabtaka da yankin tafkin Chadi, sun kudiri aniyar inganta ayyukan da za su taimaka wajen farfado ayyukan noma a yankin tafkin Chadi.

Ya ce babban abin da yake da muhimamnci a alin yanzu kara bayar da himma a dukkanin yankunan da suke makwaftaka da yankiin tafkin Chadi wajen dashen itatuwa domin hana kwararowar Hamada, wanda hakan ne ke yi babbar illa wajen kafewar ruwan tafkin Chadi.

Dangane da wannan shiri ya ce a Najeriya sun yi nisa wajen dashen itatuwa a dukanin yankuna da suke makwaftaka da yankuna masu Hamada, wanda kuma kuma sabon shirin na hadin gwiwa tsakanin Najeriya, Nijar da Chadi zai taimaka matuka wajen ganin an kai manufar da ake bukata nan da wani lokaci.