Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyar Agaji Ta International Agency Ta Dakatar Da Ayyukanta A Jihar Borno

Wannan matakin ya zo ne bayan sanarwa da rundunar soji Nigeria ta fitar ta bakin mataimakin mai hulda da Jama’a na rundunar sojin Nigeria kanar Ado Isa inda ta bukaci kungiyoyin bada agaji a jihar barno da su rufe ofisoshinsu dake birnin Maiduguri na jihar borno bayan da ka zargesu da taimakawa kungiyoyin yan ta’adda na Boko Haram da kuma ISIS da kayyakin abinci da magunguna.

Wannan mataki na bagatatan da rundunar soji ta dauka ba tare da yin wani Karin bayani ba,ya kwo tarnaki sosai game da ayyukanagaji da yaki da yunwa da ake yi da samar da abinci ga wadanda rikicin boko harama ya tagayyaraa jihar borno, kungiyar Action against hungerta samar da kayyakin abinci da magunguna ga miliyoyin mutane dake yankin Manguno da Damasak.

Idan ana iya tunawa ko a wata yuli ma kungiyar Isis ta yammacin Afrika ta yi garkuwa da daya daga cikin ma’aikata kungiyar taAction against hunger da wasu mutane 5 da suke yi masa rakiya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu