Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyar Huthi Ta Kasar Yamen Za ta Saki Fursunoni 350 Ciki Har Da Yan Saudiya 3.
A wani taronnamena labaria da ya kira a yau Shugaban kwamitin dake kula da fursunoni na kasar Yaman Abdulkadir Murtadha ya bayyana cewa tuni kungiyar Huthi ta mika fursununonin 350 da take tsare dasu ciki har da wasu yan saudiya 3, ga Majalisar dinkin duniya a wani mataki na bangare daya na aiki da yarjejniyar Sweden. 

Ya kara da cewa a yau litinin ne za’azartar da shirin karkashin kulawar majalisar dinkin duniya da hukumar bada agaji ta red cross, ganin cewa dukkansu suna daga cikin abokan tarayyar a yarjejeniyar Suweden din da aka rattaba hannun akai,
Daga karshe ya nuna cewa wannan matakin ya kara tabbatar da cewa da gaske suke yi wajen aikida wannan yarjejeniya. 

kana yayi kira ga kasar saudiya da ta dauki irin wannan mataki domin nuna kyakkkawar niyawajen aiki da yarjejeniyar Sweden kan batun fursunonin yaki da aka cimma matsaya a kai, kuma ya bukaci Majalisar dinkin duniya da ta matsa lamba kan kasar saudiya na ganin ta cika alkawarin da ta dauka.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu