Majalisar wakilan Amurka wacce zata fara bincike kan wasu laifuffukan da take tuhumar shugaban kasar Donal Trum da aikatawa, ta bukaci sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya mika mata wasu takardu wadanda zasu taimaka wajen tabbatar da laifuffukan da majalisar take zargin shuganan kasar da aikatasu, wanda kuma zai iya kaiwa ga tube shi.

A cikin wata wasika wacce kwamitin kula da lamuran harkokin wajen na majalisar ya rubutuwa Pompeo, kwamiyin ya bukace shi day a gabatar da wadannan takardun ko kuma kwamitin ya dauke shi a matsayin wadan ya ke son hana binciken tafiya.

Shaidun dai suna da nasaba da haduwa shugaban kasar ta Amurka da kuma tokoransa na kasar Ukrain, inda da yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Jor Biden zangon kasa a zabubbukanshugaban kasa na shekara mai zuwa.

Kafin haka dai majalisar ta ki amincewa da bukatar wasu yan majalisar na jam’iyyar Republican na dakatar da binciken da kuri’u 222, da kuma 184.