A wani zama da Majalisartayi , ta kafa kwamitin da zai yi nazari kan hanyar da tafi dacewa wajen aiwatar da manufar.

Shugaban masu rinjaye a majalisar Alhassan Ado Doguwa ya shaida wa manema labarai cewa matakin da Babban Bankin Najeriya ya dauka, masu kanana da matsakaitan masana’antu ne zai fi shafa.

Don haka bai dace a dora irin wannan haraji na gaira babu dalili ga ‘yan kasuwa da ke yankunan karkaraba.

Ya kara da cewa Mutane sun je sun ci kasuwar kauyuka, sai kuma ace idan sun kai kudi banki za a dora musu wannan haraji ai babu adalci anan’’

Yanzu haka dai Majalisar wakilan za ta jira sakamakon binciken kwamitin, kafin daga bisani su dauki matakin da ya dace.

A yanzu dai sun bukaci Babban Bankin Najeriya CBN ya dakatar da wannan mataki nan take.