Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

MU'ASSASATUS SHUHADA TA ZIYARCE WANDA JAMI'AN TSARO SUKA RAUNATA A GARIN KATSINA....Wakilan mu'assatus shuhada na Harkar musulunci, sun kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga yan'uwa na garin Katsina.

Malam Abdulhamid Bello ne ya jagoranci Yan'uwan zuwa markaz Katsina, inda suka yi wa Malam Yakubu Yahya Katsina jaje akan waki'ar da ya faru ranar Ashura 10-9-2019 Talatar da ta gabata.

Tawagar dai ta kuma je ta'aziyya ga Makwabcin Markaz wanda ya cika a sanadiyyar shakar tiyagas da yayi a lokacin da jami'an tsaro suka kawo hari a markazin yan'uwa na garin Katsina.

Malam Abdulhamid Bello ya mika ta'aziyyar tasu ga surukin shi mamacin, wato Mal Yakubu Idris Katsina tare da kuma Yan'uwan mamacin a cikin gida.
Daga nan kuma tawagar ta je gidan su Shahid Abubakar Sulaiman sabuwar Unguwa Katsina, daya daga cikin shahidan waki'ar Ashurah ta Kaduna, wanda shi ma a nan Sheikh Abdulhamid Bello ya yi wa mahaifin Shahidin ta'aziyya.

Mahaifin na Shahid Abubakar Sulaiman ya nuna farin cikin sa ga wannan ziyarar ta ta'aziyya da aka kawo masu, sannan kuma ya yayi addu'ar Allah ya karbi shahadar dan nasa.

Daga karshe tawagar ta mu'assasa ta kai ziyarar jajantawa ga wasu yan'uwa guda biyu da ga yankin Malumfashi da suka samu raunuka a lokacin waki'ar Ashurah ta Malumfashi, wadanda aka kawo asibitin federal medical Centre Katsina.

Kamar yadda ku ke gani a hoto

KNPRSCD 07
Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu