Mummunan shirin jami'an tsaro na afka wa markazin yan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky H na garin Katsina

Labarin da ke shigo mana a yanzu haka shine, bayan yunkurin tarwatsa taron muzaharar ashura a garin Katsina da safiyar nan, to yanzu kuma tawagar gamayyar jami'an tsaro suna yunkurin zuwa markaz ta Katsina.

A yanzu haka suna kusa da markaz din suna harbo tiyagas, amma yan'uwa sun kora su.

Sannan kuma daga wata majiya mai tushe an ji cewa suna neman bulldozers a wajen wasu masu kudin na garin Katsina, da nufin suzo markaz da karfe 3 na dare su rusa markaz.

Hasbunallahu wa ni'imal wakil,.
Muna barar addu'ar yan'uwa a kan abin da ke faruwa.

Sannan kuma al'umma su sani ga abin da wannan la'anannar gwamnati ke shirin yi.
A lokacin da suke tattaunawar sulhu da barayi masu bindiga, amma suna afkawa al'ummar da ba ta da makami.

@Kaduna Press Daga
Media forum Katsina