Tawagar ma’aikatan lafiya na 'yan-uwa Musulmi almajiran Shaykh Zakzaky (H) watau ISMA, sun kwashe kwanaki  biyu Alhamis da Juma’a da su ka gabata, su na zagayen gidajen makwabtan Markazin ‘yan-uwa da ke unguwar Kofar Marusa Sauri da wurin zuwa domin jajantawa wadanda harin ranar Ashura da Mahukuntan Nijeriya su ka kaddamar ga unguwar da mutanen unguwar.

Zagayen ya hada da kokarin kara tantance wadanda su ka samu cutuwa sosai sakamakon wannan hari na Teargas da harsasan bindiga.

Akwai makwabcin Markaz dattijo dan sama da shekara saba’in Shaheed Mallam Muhammad Adamu da wannan hayaki turnuke gidansa ya zamo ajalinsa, ’yan sanda su ka yi masa kisan gilla da hayaki mai guba a cikin gidansa.

Yayin wadannan ziyarori an binciki yanayin lafiyar makwabta da aka ziyarta, akwai masu matsaloli sakamakon shakar hayaki mai guba da yanayin da aka shiga na tsoratarwar masu kawo hari da sauransu, an gayyaci mutane da dama zuwa Sickbay ‘yar karamar asibiti a cikin muhallin Markaz aka ba su magunguna da shawarwari. An kuma jajantawa wadanda sun sami sauki sakamakon wannan ta’asa.

Ra’ayin mazauna wannan unguwa duka ya zo daya akan cewa lalle su na zaune lafiya da ‘yan-uwa musamman Mallam Yakub Yahya, kuma zasu cigaba da kasancewa tare da wannan Harka.

Alhaji Mansur Ya'u (Babba) wanda wani makwabcin Mallam ne ya sheda mana cewa a lokacin da abin ke faruwa ya kawo kudi ya baiwa matansa domin su hau abin hawa su bar unguwar amma su duka suka ce sai dai a nike su tare da Mallam, babu inda za su tafi.

Hajiya ‘Yar Fara dattijiwa yar shekara saba’in makwabciyar Markaz, tace babu inda za mu mu bari diyan banza su cimma Mallam, mun shirya su kashe mu tare da shi da ‘ya’yan mu da jikoki, tace ban taba jin karatu mai dadi irin na Mallam Yakub ba, tace, mun sheda yana layya da sadakoki saboda da Allah.

Sanata Alhaji Abdu Yandoma, yace ku gaida mani Mallam, babu wani hakuri ko jaje da Mallam zai aiko mana, an zo cutar da shine aka cuce mu, Allah Ya saka mana baki daya,

Alhaji Tukur dattijo ne sosai sama da shekara tisi’in ya ce mun sha azabar Teargas daga ‘yan-sanda, amma Allah Ya isa tsakanin mu da su, ba laifin Mallam ba ne ko almajiransa, na tafi gidan dan-uwa na, na sami labarin sun zagaye mana unguwa na dawo, yara na na cewa mu bar unguwar na ce masu babu inda zani, na ratso ta gaban ‘yan sanda na wuce har wani daga cikinsu na tambayar dattijo ina zaka? Nace masa gida na, nan ba Batsari ba ce ko Kankara me ya kawo ku?

Akwai wani bawan Allah A Mukhtar Suleiman wanda Teargas ta fada a tsakar gidansa, abin ya cutar da mu, shima ya dora laifin wannan ga wadannan ‘yan ta’adda da ya kamata su tafi dajin Batsari inda aka fi bukatar su.

Wata mata 'yar kabilar Igbo da mijinta wadanda makwabtan Mallam ne, sun yi Allah wadai da Buhari da gwamnatin sa wadanda suka kira da ‘yan ta’adda masu takura ‘yancin addinin mutanen kasa.

Zuwa yanzu an sami gidaje da dama wadanda kwanon rufin su ya farfashe da bangayen su sakamakon duwatsu da Teargas, yanzu haka ‘yan-uwa almajiran Mallam na cigaba da gyarawa wadannan makwabta muhallan su da aka lalata da duwatsu da kwafsar Teargas da harsasan ‘yan-sanda.

Daga: Sashen Lafiya na Yan-uwa Musulmi, Yankin Katsina,