da ake Wasu rahotanni daga Najeriya na cewa an kashe sojoji kimanin 13 a wasu hare-hare da ‘yan bindida  mayakan kungiyar Boko haram ne suke kaiwa a kan sojojin a cikin jahar Borno a cikin ‘yan kwanakin nan.

Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, wasu majiyoyin sojin Najeriya sun tabbatar mata da cewa, tun daga ranar Lahadin makon da ya gabata ne mayakan Boko Haram suka fara kaddamar wasu hare-haren da suka yi ajalin sojin Najeriya akalla 13 a sassa daban-daban na Jihar Borno.

Daga cikin wuraren da aka kaddamar da wadanna hare-hare a cikin wannan mako dai har da Gajigana da Kukawa da suke acikin jihar ta Borno, inda baya ga kai hare-haren 'yan ta'addan kuma sun kwashi tarin makamai.

Koacikin wannan mako dai babban hafsan sojin kasar Janar Yusuf Tukur Burutai ya ziyarci Maiduguri inda ya gana da wasu daga cikin manyan jami’an soji da suke gudanar da ayyukan tsaro a jihar, da nufin kara kaimi wajen ci gaba da fatattakar mayakan na Boko Haram.