Najeriya ta sami kudin shiga fiye da Naira Triliyan 28, ta hanyoyin da ba man fetur ba a cikin shekaru biyar

Hukumar fayyace ayyukan masana’antun kasar ta Najeriya, ( NEITI) ce ta sanar da cewa; kudaden da Najeriyar ta samu daga ayyukan da ba su da alaka da man fetur daga shekarar 2012-2016 sun kai naira tirilyon 28.58.

Kudaden shigar dai an same su ne daga harajin da ake sa wa ma’adanai,da kuma sana’oin da basu da alaka da ma’adanai, sai kuma haraji akan kamfanoni.
Kasar Najeriya dai tana kokarin ganin ta sami kudaden shiga daga hanyoyin da ba su da alaka da man fetur