Najeriya tana bukatar likitoci kimani 290,000 don cike bukatar hukumar lafiya ta duniya na yawan likitoci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto Dr Abdulkadir Tabari shugaban asbitin koyarwa na Barau Dikko da ke birnin Kaduna na tarayyarb Najeriya yana fadar haka.

Dr Tabari ya bayyana haka ne a wata kisida day a gabata a taron kungiyar likitoci ta kasa karo na 39 a ranar Alhamis a Kaduna.

Likitan ya kara da cewa a bisa kididdiga na hukumar lafiya ta Duniya Najeriya ta samar da likitoci 72,000, amma kuma likito 35,000 kacal suke aiki a cikin kasar
Rahoton hukumar ya kara da cewa najeriya tana fama da karancin likitoci sosai ta yadda likita gudana yana kula da mutane 5,700 a maimakon likita guda ga mutane 600 na hukumar.

Dr Tabari ya bayyana matsaloli wadanda suka hada da rashin aikin yi ko kuma karancin albashi ne suke hana likitoci zama a kasar