Mataimakin Shugaban Bankin Duniya mai kula da kasashen Afrika, Hafez Ghanem ya bayyana haka a lokacin da ya ke hir da manema labarai a Abuja, ya fadi cewa tattaunawa da gwamnatin Najeriya dangene da bukatar kasar ta neman bashin makuden kudade har dala bilyan 2.5. kudaden da take cewa zata yi amfani da su ne wajen inganta wutar lantarki a fadin kasar.

Har ila yau Ya kara da cewa bashin zai sa tattalin arzikin Najeriya ya rika gogayya da na manyan kasashen duniya tare da habbaka masana’antu da kuma samar wa matasa ayyukan yi.da kuma fatattakar fatara da talauci da kara inganta rayuwar jama’a dama.

Idan ba a manta ba, a cikin 2018 Najeriya ta ci bashin Dala bilyan 2.4 daga Bankin Duniya. Haka kuma bankin ya bayar da dala milyan 486 domin inganta tashoshin wutar lantarki da gyaran wasu kananan tashoshin samar da wuta.