Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya dorawa kasar Iran laifi na hare-haren da aka kaiwa kamfanin man fetur na ARAMCO mallakar kasar Saudia ba tare da gabatar da wani dalili ba.

Tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye-shiryenta da harshen larabci a Tehran ta nakalto Pompeo yana bayyana haka ne a shafinsa na twitter a jiya Asabar.

Mike Pompeo ya kara da cewa kasar Iran ce take goyon bayan mayakan Huthi na kasar Yemen wadanda suka kai hare-hare kan kamfanin na Aramco, don haka ita ce da alhakin kai hare-haren.

Daga karshe Pompeo ya ce Amurka tana kira ga kasashen duniya gaba daya su yi allawadai da kasar Iran kan wannan harin.

A wani labarin kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya ta yi allawadai da hare-haren da mayakan huthi suka kai kan kamfanin Aramco.

A daren ranar Asabar da ta gabata ce jiragen yaki wadanda ake sarrafa su daga nesa guda 10 na dakarun kungiyar Huthi a kasar Yemen suka kai hare-hare kan matatun man fetur na kamfanin Aramco a garuruwan Bakiq da kuma Haris na kasar Saudia, wadanda suka yi sanadiyyar lalata kimani kashi 50% na matatun man.

Dakarun sa kan na Alhuthi dake mara baya ga dakarun Yemen sun ce an kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa a kan al’ummar kasar Yemen, inda ta kashe dubban mutanen kasar.