Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Qarqash: Muna maraba Da Kyautata Aalaka Da IranKaramin ministan harkokin wajen kasar hadaddiyar daular larabawa Anwar Qarqash ya yi maraba da duk wani mataki na kyautata alaka da kasar Iran.

Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, a zantawar da ta yi da karamin ministan harkokin wajen kasar hadaddiyar daular larabawa Anwar Qarqash, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta sake kyautata alakarta da kasar Iran, a matsayin kasashe masu makwabtaka da juna.

Anwar Qarqash ya ce, a halin yanzu babban abin da kasashen yankin gabas ta tsakiya suke bukata shi ne fahimtar juna da kuma kyautata alaka, wanda hakan ne zai kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar Iran ta gabatar da shawara ga dukkanin kasashen yankin tekun fasha, da suka hada da hadaddiyar daular larabawa da kuma Saudiyya, kan su hada gwiwa domin yin aiki tare wajen tabbatar da tsaro a yankin, da kuma ci gaban al’ummominsu, amma wanann kira bai samu karbuwa ba.

Tun bayan kakkabo jirgin Amurka da kasar Iran ta yi a kwanakin baya, hadaddiyar daular larabawa ta aike da tawaga ta musamamn zuwa Iran domin tattaunawa, matakin da Iran din ta yi lale marhabin da shi.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu