Mutane 16 ne suka yi shahada a kasar Yemen a safiyar yau Talata bayan hare-haren jiragen yakin saudia a kan garin “Qatibah” na lardin Dhale daga kudancin kasar.

Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye-shiryenta ta harshen larabci a nan Tehran ta kara da cewa a cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai yara 7, mata 4 da kuma maza 5.

Al-Alam ta nakalto wata majiyar cikin gida ta kasar Yemen tana cewa jiragen yakin na saudiya sun kai hare-haren kan gidan wani mutum mai suna “Abbas Al-Halimi” a garin na Qatibah inda mutane 16 suka rasa rayukansu a gidan sannan wasu suka ji rauni.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa banda harin na faroko, jiragen yakin na saudia sun kai hare-hare kan yankin Sawaad a cikin lardin Umran inda a nan ba mutane 9 suka yi shahada.

A wani labarin kakakin sojojin kasar Yemen ya tabbatar da cewa jiragen yakin na Saudia sun kai hare-hare kan wurare 42 a cikin sa’o’I 12 da suka gabata a duk fadin kasar.

Hare-haren jiragen yakin saudia na yau Talata kan kasar Yemen, ya nan kamar maida martani ne ga shelanta dakatar da kai hare harekan kasar Saudiya wanda mayakan Huthi suka yi a cikin yan kwanakin da suka gabata.