Daga Malam Ibrahim Ado Kurawa

Ya Kuma Yi Alwashin Turmushe Dariqa A Masarautar Sa, Harma Ya Fara Da Cire Limamin Garin Sa Rano Daga Limancin Masallacin Rano,An kuma Hana Karanta Wazifa Da Zikirin Jumaa Masallacin.

A Lokacin Da Yan Shiga Tsakani Suka Je Domin Ganin An Sasanta Lamarin,Ya Bayyana Musu Cewa Dama Ya Dade Yana So Yayi Hakan,Harma Ya Nuna Musu Takardar Daya Rubutawa Zuwa Ga Mai Martaba Sarkin Kano,Dan Neman Sahhale Masa Hakan,Ashe ma Damar Hakan Tana Zuwa Gare Shi A Cewar Sa.

To Muna Kai Kararsa Zuwa Ga Allah,Kuma Muna Sanar Da Da Dukkan Yan Uwa Dasu Dukufa Da Addua Akan Allah Ya kwace Abinda Yake Gadara Dashi.

Muna Rokon Allah Yai Masa Abinda Yaiwa Wadanda Suka Gabace Shi Na Daga Sarakuna Masu Raayi Irin Nasa..