Gwamnatin kasar Saudiya ta saida ginin karamar ofishin jakadancinta da ke birnin Istambul na kasar Turkiya a asirce sannan tare da karya farashin ginin zuwa kashi 1/3 kacal .

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar faransa ya nakalto wata jaridar kasar Turkiya mai suna “Daily Sabah” a bugunta na jiya Talata tana cewa Saudia ta saida ginin mai hawa hude ne kwanaki 45 da suka gabata, sannan ta nakalto wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiya wanda bai bayyana sunansa ba yana fadawa wata kafar yada labarai kan cewa ba su da masaniya dangane da sayar da karamin ofishin jakadancin kasar ta Saudia.

Ya kuma kara da cewa a ka’ida dole ne gwamnatin kasar Saudiya ta nemi izinin gwamnatin kasar Turkiya, ta ma’aikatar harkokin wajen kasar kafin ta saida wurin idan har ta yi hakan.

Labarin ya kara da cewa za’a maida ofishin jakadancin na Saudia a birnin na Istambul zuwa kusa da na Amurka a wata unguwa da ake kira Istinyea a karamar hukumar Sariyer