Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Saudiyyah: Gobara Ta Tashi A Tashar Jiragen Kasa Ta Birnin Jeddah


An samu tashin gobara a tashar jiragen kasa na birnin Jeddah dake kasar Saudiya
Majiyoyin labaran kasar Saudiya sun sanar da tashin gobara a tashar jiragen birnin jeddah, tare da bayyana cewa har yanzu ba a kai ga gane musabbabin tashin gobarar ba.

Jaridar Sabak ta kasar Saudiya ta ce an dakatar da duk wani kai kawo na jiragen kasa a wannan tasha, tare kuma da kwashe dukkanin fasinjoji da ma'aikatar tashar ganin yadda gobarar ke kara ruruwa.

A nata bangare tashar talabijin din Al-arabiya ta sanar da cewa babu wani mutun da ya rasa ransa ko kuma ya jikkata sanadiyar tashin gobarar.


Post a Comment

0 Comments

Close Menu