Sayyid Hassan Nasrullah ya fadi hakan ne a wata hira daka yidashi ta gidan talbijin inda ya kara da cewa gwamantin Ali Saudi ta tsufa kuma da alama tana nunafashin karshenne na rayuwarta , saboda da dalilai masu yawa kamar matsalar manfetur da take fuskanta da ba’a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 100, da kuma yaduwar fasadi da cin hancin da rashawa a tsakanin masu rike da madafun iko a kasar.

Har ila yau ya bayyana cewa irin mataken dawannan gwamnatin take dauke ya sha banban da na wadanda suka gabaceta, wanda hakan zai kara gaggauta rushewarta ne , yana mai cewa harin da yarima mai jiran gado mohammad Bin Salm ya jagoranci kaiwa a kasar Yamen da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe zai su yi tasiri sosai ga makomar gidan sarautar ta Ali sa’ud.

Daga karshe sayyid nasrullah ya zagi kasar saudiya dakara ruruta wutar zaman tankiya tsakaninta da kasar Iran , domin ita ce ta faranuna kiyayya afili saboda irin goyon bayan da kasar Iran take bawapaladinawa game da gwagwarmayar da suke yi ta kwatar yancin su .