A jiya Litinin ne dai aka sanar da rugujewar kamfanin, tare da barin abokan cinikayyarsa 600,000ba tare da sun san makomarsu ba a kasashe daban-daban na Duniya. 

Shugaban zartarwa na kamfanin Peter Fankhauser ya bayyana takaicinsa akan rushewar kamfanin bayan da ya kasa samun lamuni daga masu bayar da bashi.
Hukumar Sufurin kasar Birtaniya ( CAA) ya sanar da cewa; Kamfanin na Thomas Cook ya daina gudanar da harkar kasuwancin da yake yi, don haka gwamnati za ta yi jigilar ‘yan kasar su 150,000 da suke watse a cikin kasashe daban-daban. 

Thomas Cook yana daya daga cikin kamfanoni mafi dadewa a harkar yawon bude ido a kasar Birtaniya. Rushewar kamfanin dai ya raba dubban mutane da aikin yi.