Wannan wata manufa ce ta kawo cikas ga kasashen China da Indiya
Muhammad Husaini Al-Heikal dan jaridar kasar Masar

Husaini Al-Heikal fitaccen dan jaridar kasar Masar da ya rasu a shekara ta 2016 shekaru biyu da suka gabata ya rubuta wani batu a cikin jaridar Al-Ahram ta Masar da a ciki ya gargadi gwamnatocin kasashen musulmi amma suka yi watsi da gargadin nasa, don haka mene ne ya faru?

A cikin wannan batu ya tabo halin tattalin arziki da kasashen yamma musamman Amurka suke ciki, yana mai nuni da cewa: Yaki daya tilo ne kawai zai iya samar da tsaban kudi dalar Amurka tiriliyan uku domin farfado da harkar tattalin arzikin kasashen yammaci da nufin hana rushewar tattalin arzikinsu, saboda a halin yanzu babu hanyar da bankunan kasar Amurka da na kasashen yammacin Turai za su iya biyan kudaden ribar ajiyar kasashen Saudiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa. Sakamakon haka suna da bukatar samar da wata hanyar kunna wutan yaki na uku a yankin gabar tekun Pasha.

Mene ne wannan manufa take dauke da shi?

Manufa ta farko kan kunna wutan yaki na uku a yankin tekun Pasha ita ce: Bayan faduwar farashin gangar man fetur daga kudi dalar Amurka 130 zuwa kasa da kasha daya cikin uku. A gefe guda kuma matakin da kasar Amurka da kasashen Turai za su dauka na kakaba takunkumi kan kasar Rasha sakamakon mamaye yankin tsibirin Crimea zai sanya kasar Rasha ta fuskanci matsalar tattalin arziki. Don haka a halin yanzu hanya daya tilo da ta dace ga makobta da suke arewaci ita ce kunna wutan yaki tsakanin manyan kasashe biyu masu arzikin man fetur a duniya wato Iran da Saudiyya.

Idan har aka samu bullar wannan yaki, to, farashin man fetur zai yi tashin gwabron zabi. Wasu manazarta suna fadin cewa farashin man fetur din zai kai dalar Amurka 200 zuwa 400 a kan kowace ganga. Ita kuma kasar Amurka za ta yi amfani da man fetur dinta a cikin gida, kuma Amurka za ta dauki matakin sayar da man fetur dinta da tsada ga kasashen da suke sayan mai daga kasashen Iran da Saudiyya. Wannan zai sanya tattalin arzikin kasar Amurka ya kara bunkasa.

Manufa ta biyu kan kunna wutan yaki na uku a yankin tekun Pasha ita ce: Samun riba mai yawa a harkar sayar da nau’o’in makamai ga kasashen da suke yaki da junansu gami da kasashen makobta da suke cikin damuwa da bukatar sayan manyan makamai masu karko.

Manufa ta uku kan kunna wutan yaki ta uku a yankin tekun Pasha ita ce: Hana ci gaban kasashen China da Indiya da suka yunkuro a duniya, inda a shekaru goma da suka gabata da daraja biyu kacal kasar Amurka da kasashen yammacin Turai suka haura su a fagen bunkasar tattalin arziki.
Kasashen China da Indiya kawai suke sayan kashi hamsin cikin dari na yawan man fetur da ake fitarwa a yankin tekun Pasha. Idan har kasashen Amurka da Rasha suka zame manyan kasashen da suke fitar da man fetur a duniya maimakon kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya ta OPEC, to babu kokwanton cewa za su dauki matakin sayar da gaggar man fetur da tsada ga wadannan kasashen biyu wato China da Indiya lamarin da zai yi mummunan tasiri a harkar tattalin arzikinsu.

A nan mene ne mahangar kasashen Iran da Saudiyya dangane da wannan makirci?

*Iran tana maganar cewa a cikin sa’o’i uku kacal za ta rusa duk wani abu mai amfani na Saudiyya a dukkanin garuruwan kasar amma banda biranen Makkah da Madinah ta hanyar makamanta masu linzami.
*Sabbin fuskokin da suka dare ragamar sarautar Saudiyya ga kuma rashin kwarewarsu kan harkokin mulki suna furuci da cewa a cikin awa guda rundunar sojin saman kasarsu za ta mamaye sararin samaniyar kasar Iran.

*Abin da zai faru a karshen lamari shi ne rusa duk wani abu mai amfani da kasashen biyu suka mallaka da kashe dubban daruruwan fararen hula da na soji a kasashen musulmi biyu Iran da Saudiyya.
*Kowace daga cikin Amurka da Rasha da kuma kungiyar tarayyar Turai tana da irin nata amfani a yakin, bayan cimma manufofinsu uku da muka ambata, a gefe guda kuma Haramtacciyar kasar Isra’ila bayan irin tallafin da za ta gabatar ga uwargijiyarta Amurka, kuma za ta zame dillaliyar sayar da makaman manyan kasashen duniya a yankin gabas ta tsakiya. Sakamakon haka karfin makamai masu linzami na Iran da karfin rundunar sojin saman Saudiyya za su ruguje lamarin da zai sanya Haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame ba ta da tsara da zai iya tunkararta a yankin.

*Kisan gillar da aka yi wa mahajjatan Iraniyawa, aiwatar da kashe- kashen gilla kan wasu ‘yan gidan sarautar Saudiyya da tsare wasu a gidajen kurkuku gami da killace wasu sakamakon kin amincewa da siyasar yakin mahukuntan kasar, sauke wasu daga kan mukamansu, rufa-rufa kan mutuwar ministan harkokin wajen Saudiyya a kasar Amurka, kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen musamman magoya bayan Husi kan zargin cewa suna goyon bayan kasar Iran, aiwatar da kisan gilla kan Sheikh Nimr, Kunna wutan kisan kiyashi kan al’umma mafi muni a duniya a watannin da suka gabata a kasar Siriya, matakin rashin hankali da dabbanci da wasu ‘yan tsiraru suka dauka na mamaye ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Tehran na kasar Iran… duk wadannan suna da ma’ana guda kuma ba sune kadai ba.

*Yaki a yankin gabas ta tsakiya karo na uku da muke tsammani ya karato mu kusa. Zabi kawai ya rage a hannun masu zurfin tunani da hankali saboda kada a sake kakaba mana wata wutar yakin.

*Shugaba Trump da mukarrabansa ba za su taba amincewa da duk wani matakin da ya gaza rusa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ko rarraba ta zuwa kasa kasa. Kawai fadaka da basira sune sharadin ci gaba da rayuwa.