Rahotanni sun bayyana cewa an bude iyakar Alqa’im ,iyaka mafi girma dake tsakanin kasashen Siriya da Iraki tun bayan da aka fatattaki kungiyar yan ta’ada ta Daesh da ada take rike dashi tun a shekara ta 2014, kuma an yi hakan ne domin bawa alumomin kasashen biyu dammar ci gaba da shige da fice tsakanin kasashen dake makwabtaka da juna.

A makon jiya ne Pira Ministan kasar Iraki Adil Abdul Mahadi ya bada umarnin bude iyakar ta al’Qa’im da ta raba tsakanin kasashen biyu bayan da suka cimma matsaya na yin aiki tare domin tabbatar da tsaro a iyakar, ita dai wannan iyaka tana da muhimmanci sosai domin ta hade lardin Al’anbar na kasar Iraki da kuma garin Bukamal dake lardin Dairiz zur na kasar Siriya.

A cikin watan Decembar shekara ta 2017 ne kasar Iraki ta kakkabe dukkan gyaron yayan kuniyar ta’adda ta Daesh ,duk da yake cewa sun ci gaba da kai hare hare daga iyakar kasar,