Rundunar sojin Somaliya, ta sanar da cewa, dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan ta'addan Al shabaab 13 a kudancin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin ya shedawa manema labarai cewa, 'yan ta'adda sun kai hari kan wani sansanin sojin gwamnati dake kudancin kasar, kuma nan da nan sojojin sun mayar da martani tare da dakile harin.

Ya ce 'yan ta'adda 13 sun mutu a musanyar wutan da suka yi da sojojin gwamnati, yayin da wasu daga sojojin gwamnati suka ji rauni.

Kungiyar Al Shabaab ta yi ikirari cewa, ta kashe sojojin gwamnati 20 a farmaki da suka kai a wannan rana.