Dakarun tsaron kasar Somaliya sun sanar a daren jiya laraba cewa sun samu nasarar kwato kauyuka uku daga hanun kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab a kudu maso yammacin kasar da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto daya daga manyan kwamandojin sojin Somaliya na cewa a wani mataki na kwato yankunan da kungiyar Ashabab ta mamaye, sojojin kasar sun samu nasarar fatattakan mayakan kungiyar ta Asbabab daya kauyukan Rahoul, da Bendub da Bywadhaly a yankin kudu maso yammacin kasar, inda suka koma karkashin ikon gwamnatin kasar ta Somaliya.

Kwamandan ya kara da cewa a yayin kai farmakin sojoji sun hallaka tare da jikkata wani da adadi na mayakan kungiyar ta'addancin ta Ashabab.

Tun a shekarar 2007 ne kungiyar Ashabab ta mamaye kasar Somaliya, to saidai a shekarar 2011, sojojin Somaliya tare da hadin gwiwar dakarun wanzar da sulhu na kungiyar tarayar Afirka sun samu nasarar fatattakar mayakan na Ashabab daga birnin Magadushu, da wasu manyan biranan kasar, inda a halin da ake ciki, har yanzu kungiyar ta Ashabab ke rike da wasu kauyuka na kudu maso yammacin kasar ta Somaliya.