Kaduna Press Media News
Kaduna Press 


A wani taron manema labaru da kakakin sojan kasar Yemen, Yahya Sari’i, ya gabatar dazu a birnin San’aa,ya bayyana cewa; Sojojin kasar sun kai wani farmaki a gundumar Najran ta kasar Saudiyya a cikin watan Ogusta da ya shude.
Kaduna-press.blogspot.com
Kaduna Press 

Yahya Sari’i ya kara da cewa; Sojoji da dakarun kai na kasar Yemen din sun kai harin ne bayan tattara bayanai akan sojojin Saudiyyar dake yankin na Najran tare da kuma shirya kwanton bauna.

Daruruwan sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korensu da su ka kai 500 sun halaka, yayin da aka kama wasu daruruwa a matsayin fursunoni.

Har ila yau Yahya Sari’i ya ce; A wannan tsakanin sojan saman kasar sun kai hare-hare da jirage marasa matuki har sau 20 a cikin wurare daban-daban da su ka hada da birnin Riyadh.

A wani sashe na bayanin da ya gabatar a taron manema labarun, Yahya Sari’i ya ce; adadin sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korensu da su ka kashe sun kai 500, Wadanda kuma suka kama sun haura 2000.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani mayar da martani da ya fito daga kawancen da Saudiyyar take jagoranta akan taron 

manema labarun sojojin kasar ta Yemen.
Yakin kasar Yemen dai ya shiga shekara ta biyar wanda a wannan tsakanin ya ci rayukan mutanen kasar ta Yemen da dama.