Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Tunisia: Kashi 45% Ne Na Mutane Suka Gudanar Da ZabeHukumar zaben kasar Tunusiya ta sanar da cewa kashi 45,2 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri’a suka fito zabe a kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar bayan rufe runfunar zaben a jiya, Hukumar zaben Tunisiya ta ce ba ta ji dadin yadda jama'a da dama suka ki fita domin ka'da kuri'u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan Lahadin ba, duk kuwa da kiraye-kirayen da shugabanta ya yi musamman ga matasa.

Gabanin zaben dai al'ummar kasar sun bukaci sabon shugabancin da za a samu ya magance matsalar tattalin arziki da kuma rashin aiki tsakanin matasa.

Hukumar zaben Tunusiyan ta ce kashi 45,2 cikin dari ne suka fito zabe, kuma idan aka kwatanta yawan al'ummar kasar da suka kai miliyan 11 da dubu 530, kimanin mutune miliyan 7 da dubu 500 ne suka cacanci yin zabe a kasar.

A nasa bangare tsohon shugaban kasar Tunusiya Moncef Marzouki ya bayana amincewarsa da shan kayi a tsakanin 'yan takarar kasar da adadinsu ya kai 26.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar Tunusiya , daga cikin 'yan takarar da suka tsaya, idan ba a samu wanda ya samu kashi 50% daga cikin yawan kuri'un da aka kada ba to dole ne a sake zuwa zabe zagaye na biyu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu