Kungiyar tarayyar Turai ta yi barazanar ficewa daga yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015 wacce aka fi saninta da JCPOA idan har kasar Iran bata koma kan aiwatar da cikekken yerjejeniyar nan da watan Nuwamba mai zuwa ba.

Jaridar The Guadian ta kasar Britaniya ta nakalto majiyar kasashen turai ukku wadanda suka rattabawa yerjejeniyar hannu, watom Faransa, Jamus da kuma Burtaniya suna fadar haka.

Kasashen sun kuma kara da cewa idan Iran ta dauki mataki na hudu a tsarinta na jingine aiki da yerjejeniyar a ranar 7 ga watan Nuwamba mai zuwa to kuwa kasashen ba su da zabi in banda yin watsi da yerjejeniyar gaba daya.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar Iran ta dauki matakai har sau ukku na jingine yerjejeniyar ko rashin aiki da ita, bisa mataki matakai, saboda gazawar kasashen na Turan wajen cika alkawullan guda 11 da suka dauka, bayan ficewar Amurka daga cikin yerjejeniyar a shekara da ta gabata.

A halin yanzu dai Iran zata dauki mataki na 4, na jingine yerjejeniyar a ranar 7 ga watan Nuwamba mai zuwa idan har kasashen na turai sun kasa cika alkawulan da suka dauka dangane da yerjejeniyar.

Bayan ficewar Amurka daga yerjejeniyar a shekara ta 2018 ta sake maida dukkan dukkan takunkuman tattalin arzikin da ake daukewa Iran saboda yerjejeniyar a shekara ta 2015, sannan ta kara wasu takunkuman don tilastawa Iran sake bude sabuwar tattaunawa kan shirinta na makamashin nukliya da kuma makamanta masu linzami