Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ( UNICEF) ya yaba da nasarar da ake samu dangane da ilimin mata a arewacin Najeriya.

A Jiya Asabar ne Asusun na kananan yara, ta bakinsa shugabarsa Euphrates Wose ya bayyana cewa; Bangare na uku na shirin ilimantar da ‘yan mata ya sami nasara a jahohin kano, katsina, sokoto, Zamfara, Bauchi da Niger.

Wose ta shaidawa kamfanin dillancin labarun Najeriya (NAN) cewa;Manufar shirin ilimantar da ‘yan matan shi ne, samarwa da mafi yawancinsu ilimi na share fage.

Bugu da kari, shugabar Asusun na kananan yara na Majlisar Dinkin Duniya ta yabawa gwmnatin jahar Sokoto saboda yadda ta samar da kudaden da ake bukatuwa da su, domin tafiyar da shirin, tana mai bayyana fatanta na ganin gwanatin jahar Kebbi ma ta bi baya
Wose ta kuma ce; Ya zuwa yanzu iyaye da dama sun fahimci cewa baya ga ilimi na addini da yake da muhimmanci ga kananan yara, samun kwarewa ma a fagen rayuwa ma yana taimakawa.