Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wasu Masu Kiyayya Da Muslunci Sun Kai Farmaki Kan Wani Masallacin A HollandWasu masu tsattsauran ra’ayin kin addinin mulsucni sun kai farmaki kan wani masallaci a kasar Holland.

Shafin yada labarai na jaridar Daily Sabah ya bayar da rahoton cewa, ‘ya’yan wata kungiya mai kiyaya da addinin muslunci a kasar Holland, sun kai farmaki a kan wani masallaci a garin Almara.

Rahoton ya ce mutanen sun yi rubuce-rubucen batunci akan addinin muslunci a kan bangayen masallacin, tare da yi kalamai na batunci a kan musulmi da musulunci, tare da kafa tutoci a bakin masallacin masu dauke da rubutun batunci ga muslucni, amma ba su taba musulmin da suke cikin masallaci ba.

Kungiyar (Rechts in Verzet) mai tsatsauran ra’ayin kin jinin muslucita sanar ad cewa ita ce take da alhakin kai wannan farmaki, kamar yadda ta sanar a shafukan yanar gizo da take saka bayananta.

Masu kula da masalalcin sun bukaci mahukuntan kasar ta Holland da su dauki matakin basu kariya da kuma hana faruwar irin hakan.

A cikin shekara ta 2018 maan kai wani farmaki kan masallacin Amir Sultan da ke birnin Amstardam, inda kungiyar ta dauki alhakin kai harin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu