Babar kotun koli ta kasa dake birnin Abuja ta bada umarnin a ci gaba da tsare shugaban kamfanin sahara reporters da ya jagoranci zanga zangar neman sauyi a nigeria wato Revolution Now tare da abokinsa a hannun jami’an tsaro na farin kaya wato DSS har zuwa lokaci da za ta saurari karar day a shigar ne neman a bashi beli.

Alkalin kotun mai sharia Ijukwu Ojoku ya sanya ranar Juma’a a matsayin ranar da zai yane hukumci kan bukatar day a gabatar na nemana bad abelinsa, wannan ya biyo bayan gurfanar dasu da ka yi a gaban kuton ne da da zarge –zarge guda 7 da suka hada da cin amanar kasa, da dai sauran laifuffuka da gwamnatin tarayya ta gabatar akansu. Sai dai wadanda ake zargin sun yi watsi da dukkan zarge –zargen.

Daga karshe lawyan dake kare Sowore din Adeyinka Olumide –fusika ya bukaci kotun da tabawa Sowere dama ya yi amfani da belinsa da mai sharia Taiwo Taiwo ya bayar tun a ranar 24 ga watan satumba, kana ya bukaci a bada belin abokin sowere din da ake tsare dasu, sai dai alkalin kotun yayi watsi da wannan bukatar.