A taron koli na MDD, karo na 74 da aka fara, a birnin New York, kallo ya koma kan ganawar da ake zaton zata iya wakana tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da kuma Shugaban kasar Iran Dakta Hassan Rohani.

Shugaban kasar Faransa Emmaniel Macron, wanda ke son ganin shuwagabannin kasashen biyu sun gana a wani mataki na kwantar da hankali dangane da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya dama zaman tankiya dake tsakanin Amurka da Iran, ya ce ya samu ganawa da shuwagabannin biyu daban-daban a jiya Litini.

Mista Macron ya kuma bayyana ‘yan jarida cewa zai sake ganawa da shugaban kasar ta Amurka yau Talata, duk a kokarin da yake na ganin tattaunawa ta samu tsakanin shuwagabannin domin samar da wata mafita ta kwantar da hankali mai daurewa da kuma samar da tsaro a yankin.
Tunda farko dai kafin ya isa birnin na New Work, shugaba Macron ya ce yana da yakinin cewa wani abu komi kankantarsa zai iya faruwa.

Saidai a baya bayan nan dukkan kasashen biyu sun kore duk wata yiyiwar ganawa ta tsakanin shugabanin wato Trump da kuma Rohani, inda ko a jiya shugaba Trump ya ce babu wata ganawa da aka shirya tsakaninsa da shugaban na Iran.

A cen baya dai ita ma Iran ta ce babu yiyuwar wata ganawa tsakanin ta Amurka, mudin Amurka bata janye wa kasar takunkuman zaluncin data kakaba wa kasar, bayan ficewarta daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita a shekara 2015.