‘yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen, sun ce a shirye su ke su yi sulhu su kuma dakatar da kai hare-hare kan Saudiyya mudin ta nuna cewa da gaske ta ke.

A wani jawabi daya gabatar a yayin zagayowar ranar kwace birnin Sanaa a watan Satumban 2014, shugaban majalisar siyasa ta ‘yan Houtsis, Mehdi Machat, ya ce, zasu dakatar da duk wani irin hari zuwa Saudiyya, idan har ta nuna da gaske ta ke wajen kulla zaman lafiya.

Saidai a cewarsa ana bukatar masu shiga tsakani domin kulla wajen shirin na zaman lafiya mai daurewa wanda kuma zai shafi kowa da kowa.

A ranar 14 ga watan Satumban ne ‘yan Houtsis suka dauki alhakin kai hari kan matatun man fetur na kamfanin mai na ARAMCO a Saudiyya, wanda ya hadassa hauhawan farashin dayen mai da kuma tayar da hankalin duniya.