Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ba za ta iya kammala yakin yanar gizo da ta fara da Iran ba.

Zarif ya bayyana haka ne a wata hirin da ta hada shi da tashar talabijin ta NBC ta kasar Amurka a cikin wani shirinta mai suna “Meet the press”, wanda za’a watsa cikekken hirar a yau lahadi a tashar.

Ministan ya kara da cewa a halin yanzu akwai yaki a yanar gizo da ke gudana tsakanin kasar Iran a bangare guda, da kuma Amurka da HKI a dayan bangaren, wanda da a ce sun sami nasara a yakin da kuwa miliyoyin mutane kasar Iran ne zasu rasa rayukansu.

Jaridar Washington post ta bayyana cewa, a shekara ta 2012 ne sojojin Amurka da HKI suka samar da wani “virus na yanar gizo” mai suna “Stuxnet” da nufin wargaza shirin makamashin nukliyar kasar Iran da ke Natanz.

A lokacinda yake amsa tambaya dangane zaben shekara ta 2020na Amurka kuma, shin Iran tana son shigar da kanta cikin harkokin zaben na Amurka? Ministan ya ce , ba ruwan gwamnatin kasar Iran da zabubbukan Amurka, kuma ba ta shiga cikin al-amuran cikin gida na wata kasa.