Ministan harakokin wajen Iran Muhamad Javad Zarif ya soki matsayar Amurka kan harin da dakarun kasar Yemen suka kai kan cibiyoyin man fetir din Saudiya, inda ya ce yamaniyawa sun kai harin daukan fansa kan kisan gillar da aka kwashe sama da shekaru 4 ana aiwatarwa kan al’ummarsu ta hanyar kai hari kan cibiyoyin sarrafa man fetir na kasar Saudiya.

Yayin da yake tattaunawa da Tashar CGTN mallakain kasar Sin a birnin New York na kasar Amurka, Zarif ya ce a maimakon suka kai hari kan fararen hula na kasar Saudiya, dakarun kasar Yemen sun kai harin daukan fansa na kashe duban fararen hula na kasar Yemen, a kan cibiyoyin man fetir ba tare da kashe ko da mutum guda ba.

A bangare guda kuma, Zarif ya yi watsi da zargin da kasar Amurka ta yi wa kasarsa na cewa kasar Iran din na da hanu wajen hare-haren da dakarun kasar Yemen suka kaiwa cibiyoyin man fetir din kasar Saudiya, inda ya ce a tunanin hukumomin birnin Washington kai harin kan cibiyoyin mai, abu ne da ba za a amince da shi ba, a bangare guda kuma suna taimakawa wajen yiwa duban fararen hula kisan gilla a kasar ta Yemen.

Zarif ya tabbatar da cewa Iran bata da hanu a harin da kai kaiwa cibiyoyin sarrafa man fetir na kamfanin Aramco a kasar Saudiya, to amma dakarun tsaron Yemen din da mayakan sa kai na kungiyar Ansarullah sun zabi kai harin ramuwar gayya ne a kan cibiyoyin man fetir ba gidajen fararen hula, ko asibitoci ko makarantu ba, a kisan gillar da aka kwashe sama da shekaru 4 ana yiwa ‘yan kasar su, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan yamaniyawa kimanin dubu dari, da kuma rusa duban gidajen hula da cibiyoyin kiyon lafiya da makarantu gami da wuraran ibadu da masa’antu.