A Zimbabwe, yau Asabar ne aka binne tsohon shugaban kasar mirigayi Robert Mugabe a mahaifarsa dake ta Kutama dake arewa maso yammacin kasar.

An binne marigayin ne tare da halartar daruruwan mambobin iyallensa da kuma makusanta, kamar yadda kamfanin dilancin labaren AFP, ya rawaito.

Bayanai daga kasar sun ce an dauki tsauraran matakan tsaro a mahaifar mirigayin a daidai lokacin da iyalansa ke shirin binne shi.

A ranar 6 ga watan Satumba nan ne tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe R. Mugabe, wanda ya yi fafutukar samar wa da kasar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya, ya rasu yana mai shekaru 95, bayan doguw