Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ziyarar Manzon Musamman Na Afrika Ta Kudu A NajeriyaShugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya gana da jakadan shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu a fadar shugaban kasa ba tare da halartar yan jaridu ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa jakada na musamman na kasar Afrika ta kudu Mr Jeff Radebe, tare da rakiyar jakadan Afrika ta kudu a Abuja Bobby J. Moroe, bayan saukarsa a Abuja kai tsaye ya je fadar shugaban kasa don gabatar masa uzurin gwamnatin Afrika ta Kudu kan rikicin nuna bambanci day a faru a wasu wurare a kasar wanda ya kai ga kisa da kuma lalata dukiyoyin wasu yan kasashen Afrika.

A makon da ya gabata ne shugabaya aike da jakada na musamman zuwa kasashe 6 daga cikin kasashen Afrika don basu hakuri kan abinda ya faru a kasar na cutar da yan kasashensu a Afrika ta kudu.

Post a Comment

1 Comments

Auwal Albarnawy said…
Masha Allah, Allah ya kara muku basira. Abin ya burgeni
Close Menu